Rundunar samar da lumana a Kwango

Rundunar samar da lumana a Kwango
Duk da cewa sanarwar da shugabannin gabashin Afirkan suka fitar ba ta ambaci tura wa da dakarun Ruwanda a cikin rundunar zuwa Kwango ba, amma Kwangon ta dage kai-da-fata cewa ba ta maraba da sojojin Ruwanda.

Shugabannin kasashen gabashin Afirka sun sanar da kammala shirin tura runduna ta musamman da ta kunshi dakarun kasashen zuwa gabashin Jamhuriyar Dimukurdiyyar Kwango mai fama da fitintinu. Sanarwar da gwamnatin kasar Kenya ta fitar a kan lamarin, ta bukaci Kwango da Ruwanda da ke yaki da juna a kan iyakarsu da su yi gaggawar tsagaita wuta. 

Mahukuntan Kinshasa na Kwango da masu fada-aji na Kigali da ke Ruwanda sun kwashe 'yan makonni suna jifan juna da bakaken maganganu a kan zargin juna wurin tallafa wa kungiyar 'yan tawayen M23 mai halaka fararen hula da jami'an tsaron kasashen biyu makwabtan juna. 

Zaman doya da manja tsakanin kasashen biyu dai ya yi muni ta yadda har suka fara kai wa junansu hari da makami a cikin wannan wata.


News Source:   DW (dw.com)