Rufe wa Jamus makamashi

Rufe wa Jamus makamashi
Hukumomin Rasha sun sanar da rufe bututun samar da iskar gas da ke hada kasar da Jamus bisa dalilan aikin inganta bututan na shekara-shekara.

Kamfanin da samar da isakar gaz din Rasha ne ya tabbatar da haka, inda yace katsewar za ta fara aiki daga wannan Litinin har zuwa tsawon kwanaki 10 masu zuwa, duba da muhimmancin aikin da zai yi wa bututan na Nord Stream 1 da suka ratsa tekun baltik.

Sai dai matakin na cigaba da haifar da fargaba a zukatan alummar Jamus da ke tsoron ko Rasha ka iya toshe hanyoyin samar wa Jamus din makamashin bayan kammala aikin, bisa dalilai na takon sakar diflomasiyya da ta barke tsakaninsu tun bayan soma mamayar Rasha a makwabciyarta Ukraine.

Gwamnatin Jamus ta kulla yarjejeniyar samar da makamashi da takwararta Jamhuriyar Chek a wani mataki na kandagarki.


News Source:   DW (dw.com)