A cikin tattausar lafazi Mr. Habeck ya shaidawa manema labarai cewa jam'iyyar The Green ta fadi kasa warwas da kashi 11.6 bisa 100 sabanin tagomashin da jam'iyyar ta samu a zaben 2021, inda ta samu kashi 14.7 bisa 100. Ya kuma kara da cewa wannan ba sakamako bane mai kyau da jam'iyyar za ta yi tinkaho da shi.
Karin bayani: Jam'iyyar the Greens, na son sake sabon lale
Rashin nasarar jam'iyyar Greens na nufin cewa Robert Habeck zai rasa mukaminsa a gwamnati, kasancewar Friedrich Merz na kawancen jam'iyyar CDU/CSU shi ne zai kafa gwamnati tare da kawancen jam'iyyar SPD ta Shugaban Gwamnatin Jamus mai barin gado Olaf Scholz.
Karin bayani: Jamus: The Greens ta amince da shirin kafa gwamnati
Mr. Habeck da sauran jagororin jam'iyyar The Greens sun yi amannar cewa duk da rashin nasarar da jam'iyyarsu ta fuskanta a zaben, ta dara jam'iyya mai mulki ta SPD wacce ta samu mummunar koma baya a tarihinta.