Rikicin gungun 'yan daba a kasar Haiti ya halaka mutane 5,600 a shekarar 2024 da ta gabata, karin 1,000 a kan wadanda aka kashe a shekarar 2023, yayin da wasu dubbai suka samu raunuka da kuma wadanda aka yi garkuwa da su, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar a Talatar nan.
Karin bayani:'Yan bindiga sun bude wuta kan jirgin MDD a Haiti
Shugaban hukumar kare hakkin 'dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya Volker Turk, ya ce wannan kididdiga na nuna irin munin halin jin kai da taskun da al'ummar kasar Haiti ke ciki, wadda 'yan daba ke rike da ikon mafi yawancin yankunata, ciki har da Port-au-Prince babban birnin kasar.
Karin bayani:Rukuni na biyu na 'yan sandan Kenya na shirin zuwa Haiti
Wannan tashe-tashen hankula na ci gaba da faruwa a Haiti, duk kuwa da jami'an tsaron kasar Kenya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya.