Rikicin Kwango ya ci gaba da ruruwa

Ministar harkokin wajen kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, Therese Kayikwamba Wagner ta nuna takaicin rashin samun mataki mai karfi na kasashen duniya kan 'yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan kasar Ruwanda, wadanda suka kwace iko da wasu sassan gabashin kasar. Ta bayyana haka lokacin ganawa da takwaranta na kasar Beljiyam, Maxime Prevot a birnin Brussels fadar gwamnatin kasar ta Beljiyam inda take ziyara. Ministar ta ce kimanin sojojin Ruwanda 4,000 suka kutsa Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

Karin Bayani: Tabarbarewar jinkai a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoGabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Jia Nan/Imago

Tuni kasar Beljiyam ta bukaci ganin kungiyar Tarayyar Turai ta dauki mataki kan kasar Ruwanda saboda goyon bayan 'yan tawayen na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

Kalaman na zuwa lokacin da 'yan tawayen suka yi ikirarin sake kwace wani garin na gabashin kasar, abin da dakarun gwamnati suka musanta. Haka kuma ya karyata ikirarin 'yan tawayen M23 na tsagaita wuta.

 


News Source:   DW (dw.com)