Rikicin Kwango na kara raba fararen hula da matsugunansu

Rikicin Kwango na kara raba fararen hula da matsugunansu
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutum dubu 72 sun rasa matsugunnensu a sabon rikicin da ya barke a tsakanin dakarun sojin Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango da 'yan tawayen M23.

A sanarwar da hukumar ta fidda, ta kara da cewar wadanda suka kauracewa matsugunensu a yankin Kivu na fuskantar barazanar cin zarafi da ma shiga gidajensu ana musu sace-sace.

Hukumar 'yan tawayen na M23 sun jima suna cin karensu babu babbaka a gabashin Kwangon, kuma ana zarginsu da sake tada zaune tsaye a kasar da ta jima tana fama da rikicin kabilanci. Ya zuwa yanzu akalla fararen hula dubu 170 ne ke gudun hijira tun bayan barkewar rikicin a shekarar 2021.

Dangantaka tsakanin Kwango da Ruwanda na kara yin tsami wanda ya samo asali tun bayan kisan kiyashin da aka yi a Ruwanda a shekarar 1994. 
 


News Source:   DW (dw.com)