Rikicin kabilanci ya barke a Sudan

Rikicin kabilanci ya barke a Sudan
Rikicin kabilanci tsakanin Hausawa da 'yan kabilar Brita da ke lardin Qissan a kudancin kasar Sudan ya yi sanadiyar rayukan mutane sama da 65.

Rikicin na yankin Blue Nile da ko baya ga wadanda suka rasa rayukansu wasu sama da 150 sun sami munanan raunuka a cewar wani babban jami'in lafiya da ke yankin.

Tashin hankalin dai ya fara ne bayan kisan wani manomi a farkon makon da ya gabata wanda a jiya lamarin ya yi kamari har ya kai ga sare-sare da wuka.

Yanzu haka mutane 15 da ke kwance cikin wani hali na rai kwakwai mutu kwakwai ana bukatar maida su babban asibiti da ke khartoum domin ceto rayuwarsu.

Wannan dai shi ne rikicin kabilanci mafi muni da kasar ta Sudan ke fuskanta a baya-bayan nan. Tuni gwamnan lardin Ahmed al-Omda ya kafa dokar ta baci tare da hana duk wani taron gangami ko haduwar jama'a har sai abinda hali yayi.
 


News Source:   DW (dw.com)