Gwamnan yankin Bakari Midjiyawa a sanarwar da ya fitar ya cerikiciya kaure ne bisa zargin satar dabbobi a tsakanin kabilun Moussey da Massa da suka jima suna cudanya da juna, lamarin da ya jikkata mutane kimanin 10 baya ga ukun da rikicin ya yi ajalinsu. Ya ce tuni suka jibge jami'an 'yan sanda domin dawo da doka da oda, amma kawo yanzu an rufe makarantu da kasuwanni da sauran harkoki a yankin har sai al'amura sun daidaita.
Kafar yada labaran CRTV ta ruwaito a ranar Litinin cewa kisan da aka yi wa wani dan kasuwa dan kabilar Massa da ya je sayen akuyoyi ne a wata kasuwa, ya fara tayar da rigimar da gwamnatin ta ce talauci ne ya haddasa ta, inda jami'an gwamnatin ke cewa akwai bukatar mutanen yankin su ba su hadin kai wajen yaki da fatara don samar da ci-gaba a maimakon yakar juna.