Rikici kwallon kafa ya halaka mutane 100 a kasar Guinea

Likitoci a kasar Guinea sun tabbatar da mutuwar kimanin mutane 100 sanadiyyar barkewar rikici tsakanin magoya bayan kungiyoyin kwallon kafar kasar da yammacin Lahadi, lokacin da ake tsaka da wani wasa da aka shirya don karrama shugaban mulkin sojin kasar Janar Mamadi Doumbouya.

Karin bayani:Guinea ta sanar da gudanar da zaben raba gardama

Likitocin  wadanda suka nemi a sakaya sunayensu, sun tabbatarwa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa asibitin birni na biyu mafi girma a kasar wato N'Zerekore ya cika makil da gawarwaki, wasu ma yashe a kasa, sakamakon cikar wuraren adana gawarwakin.

Karin bayani:Juyin mulki a Afrika gazawar dimukuradiyya

Wasu fayafayan bidiyo da aka rinka yadawa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda fusatattun masu kallon wasan suka rinka gwabzawa da juna, har ma suka fantsama kan titunan birnin tare da kona ofishin 'yan sandan garin, don nuna fushinsu kan wani hukuncin da alkalin wasan ya yi a lokacin da kungiyoyin biyu ke fafatawa.

Mr Doumbouya ya dare kan karagar mulkin kasar ne bayan hambare shugaba Alpha Conde a shekarar 2021, lokacin yana da mukamin Kanar na soja, kuma babban jami'in kula da lafiyar Mr Conde.


News Source:   DW (dw.com)