Matsalolin tashe-tashen hankaula a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango gami da katse tallafin jinkai da Amurka ta yi wa kasashe masu tasowa ake sa ran za su dauki hankalin shugabannin kasashen Afirka a taron da za su gudanar cikin wannan makon a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, sannan kuma za a zabi sabon shugaban hukumar gudanar kungiyar.
Karin Bayani: Shugabannin Afirka sun bukaci tsagaita wuta a DRC
Kungiyar mai mambobin kasashe 55 za ta gudanar da taron daga ranar Jumma'a mai zuwa a birnin Addis Ababa da ke zama helkwatar kungiyar. A baya an zargi shugabannin da fitar da sanarwar da suka gaza daukan matakan da za su aiwatar da abubuwan da suka amince a kai.
Yanzu haka 'yan tawayen na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na kungiyar M23 da ke samun goyon bayan kasar Ruwanda sun rufe sansanonin 'yan gudun hijira tare da tarwatsa fiye da mutane dubu-110 wadanda suka rasa matsuguni, tun lokacin da 'yan tawayen suka kwace birnin Goma.