Kimanin yara milyan uku a kasashen yammaci da tsakiyar Afirka ba sa iya zuwa makaranta sakamakon rikice-rikicen da ke faruwa a yankunan. Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da makarantu dubu-14 aka rufe a zangon farko na wannan shekara ta 2024 cikin kasashe 24 na yankunan biyu.
Karin Bayani: Najeriya: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da daliban jami'a
Haka ya nuna cewa alkaluman sun haura na bara da fiye da dubu-daya. Kasashen Burkina Faso, da Mali, da Kamaru, gami da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango suke kan gaba na matsalolin da ake fuskanta.
Majalisar Dinkin Duniya ta kara da cewa yara kimanin milyan-57 da ya dace ace suna zuwa makaranta tsakanin shekara 5 zuwa shekaru 14 na haihuwa a kasashen na yammaci da tsakiyar Afirka ba sa zuwa makaranta. Rikice-rikice da da matsalolin tattalin arziki ke kan gaba wajen haddasa matsalolin rashin zuwa makaranta a yankunan da ke nahiyar Afirka.