Rasha za ta tsagaita wuta a Mariupol

Rasha za ta tsagaita wuta a Mariupol
Ana sa ran Rasha ta fara tsagaita wuta a ma'aikatar sarrafa karafa ta Azovstal da ke birnin Mariupol na kasar Ukraine da ta yi wa kawanya don bai wa fararen hula damar tserewa.

Hukuncin tsagaita wuta na tsawon kwanaki uku da Rashar ta yi na zuwa ne bayan da Hukumar Tarayyar Turai ta fara muhawa kan kakaba takunkumi ga man kasar, mataki mafi tsauri da hukumar ke shirin dauka tun bayan da Moscow ta kaddamar da mamaya a Ukraine.

Shugabar hukumar Ursula von der Leyen ta ce kungiyar EU za ta katse samar da danyen mai daga Rasha cikin watanni 6 da kuma tattace zuwa nan da karshen wannan shekarar, hukuncin da ka iya yin mummunan tasiri ga fitar da iskar gas dinta.

Kungiyar Tarayyar Turai ta kuma yi alkawarin kara yawan goyon bayan da ta ke bai wa Maldova da ke makwaftaka da Ukraine, inda ake fargabar hare-haren a yankin 'yan awaren da ke samun goyon bayan Rasha ka iya fadada.
 


News Source:   DW (dw.com)