Rasha za ta bude hanyoyin jin kai

Rasha za ta bude hanyoyin jin kai
Rasha ta ba da shawarar bude hanyoyin jin kai don kwashe fararen hula da suka fake a wata masana'anta a Severodonetsk, wani muhimmin birni a cikin Donbass da ke a gabashin Ukraine.

Ma'aikatar harkokin tsaron Rasha ta ce za a bude hanyar jin kai zuwa arewa zuwa birnin Svatove a ranar Larba 15 ga watan Yuni daga karfe biyar na safe zuwa karfe biyar na yamma. Har sai an tabbatar an kwashe dukkan fararen hula. A cewar hukumomin Ukraine mutane 540 zuwa 560  suka fake a karkashin kasa a cikin  wani kamfanin.

 


News Source:   DW (dw.com)