Wani mutum ya bude wuta a wata makarantar renon yara da ke yankin Ulyanovsk da ke tsakiyar kasar Rasha, inda ya kashe yara biyu da malama daya kafin ya kashe kansa. Kamfanonin dillancin labaran kasar sun ruwaito cewa dalilin harbe-harben da ya rasa nasaba da rikicin iyali.
Harbe-harbe a makarantu a kasar Rasha sun fara zama ruwan dare a shekarun baya-bayan nan, lamarin da ta kai shugaban kasar Vladimir Putin ga tsananta dokar da ta shafi mallakar makamai. ko da a watan Satumbar 2021, wani dalibi dan shekara 18 ya bude wuta da bindiga a jami'ar Perm da ke Urals, inda ya kashe mutane shida tare da raunata kusan 30. Yayin da a watan Mayun bara kuwa, wani matashi dan shekara 19 ya yi harbe-harbe a tsohuwar makarantarsa, inda ya kashe dalibai bakwai da malamai biyu.