Rasha ta soke hulda da Gazprom Germania

Rasha ta soke hulda da Gazprom Germania
Rasha ta kakaba takunkumi kan Gazprom reshen Jamus da wasu tsoffin rasa na kamfanin iskar gas mallakin gwamnati tare da jimlar kamfanoni 31 wadanda Rasha ta soke yin mu'amula da su.

Shugaban Rashar Vladmir Putin ya  ba da umarnin haramta yin kasuwanci da kafanonin na Jamus wanda ya ce bai kamata a ci gaba da yin kasuwancin iskan gas din da su ba. An sanya Gazprom reshen Germany ƙarƙashin ikon gwamnatin Jamus a farkon watan Afrilu da ya gabata. A halin da ake ciki gwamnatin Jamus ta jaddada cewar tana da wadataccen iskan gas kawo yanzu, sannan ta ce babu abin tayar da hankali a ciki.


News Source:   DW (dw.com)