Rasha ta mamaye masana'antun Ukraine

Rasha ta mamaye masana'antun Ukraine
Mamayar birnin Sievierodonetsk din dai na cikin kutsen da Rasha ta kwashe watanni tana yi wa Ukraine. Kawo yanzu dakarun da Moscow ta turo Ukraine tuni saka ragargaza birnin mai dimbin tarihi.

Dakarun Rasha sun dira a wani yanki na birnin Sievierodonetsk mai rukunin kamfanoni da masana'antu a arewa maso gabashin Ukraine. Gwamnan yankin Luhansk, Serhiy Haidai, inda wannan birni yake ne ya sanar da hakan.

Bayanai sun ce kawo yanzu dakarun Rasha ne ke iko da kaso 80 cikin 100 na birnin. Rahotanni sun ce bangaren da kamfanin sarrafa sinadarai na Azot yake ne kawai ya rage a hannun dakarun Ukraine. 


News Source:   DW (dw.com)