Rasha ta sanar da kara kwace iko da wasu kauyuka biyu da ke yankin Donetsk, wanda ya ba ta damar kara kutsa kai zuwa dab da tsakiyar yankin Dnipropetrovsk. Fadar Kremli ta Rasha ta ce babban abin da take burin cimma shi ne, kwace iko da dukannin yankunan Donetsk da Lugansk da Kherson da kuma Zaporizhzhia, wadanda ta yi ikrarin mamaye wa ba tare da samun cikakken iko da su ba.
Karin bayani: Rasha ta zafafa hare-hare kan Ukraine
Kawo yanzu dai a hukumance, Rashar ta yi ce ta kwace iko da yankin Dnipropetrovsk ba. Gwamnatin Moscow dai na ci gaba da fafutukar kwace iko da karin yankunan Ukraine yayin da take tatattaunawa da Amurka kan yadda za a kawo karshen yakin Ukraine. Tun dai bayan da ta kaddamar da mamaya a Ukraine a watan Fabarairun shekarar 2022, Rasha ta yi kokarin kwace birnin Kyiv,sai dai kuma rashin nasararta na yin hakan ya sanya ta umurci dakarun kasar da su kwace iko da yankuna hudu da ke yankunan kudu da kuma gabashin kasar.