Rasha ta katse sayar wa Finland da Iskar Gas

Rasha ta katse sayar wa Finland da Iskar Gas
A wani sabon salon tsama ta diflomasiyya, hukumomi aFinland sun bayyana cewa Rasha ta katse samar da iskar gas da take sai da wa kasar. Matakin ya shafi har da Estonia.

Kamfanin da ke hada-hadar gas a Finland wato Gasum, ya tabbatar da katsewar makamashin wanda ke bi ta bututun da ya ratsa kasashen yankin Baltic da ya hada da Finland din da ma kasar Estonia.

Tun da fari dai kamfanin na Gasum ya ki amincewa ne da ya batun ci gaba da biyan kudin iskar ta gas da kudin kasar Rasha wato Ruble.

Matakin katse cinikayyar makamashin ya zo ne daidai lokacin da kasar Finland ke gab da shiga kungiyar tsaro ta NATO.

Finland din dai ta kuduri aniyar shiga kungiyar ne, bayan mamayar da Rasha ta yi wa kasar Ukraine.


News Source:   DW (dw.com)