Rasha ta katse gas ga Bulgeriya da Poland

Rasha ta katse gas ga Bulgeriya da Poland
Sakamakon takaddama kan kutsen da Rasha ta kaddamar a Ukraine, kamfanin man Rasha ya katse tura iskar gas zuwa kasashen Poland da Bulgeriya.

Kamfanin mai na kasar Rasha ya katse tura iskar gas zuwa kasashen Poland da Bulgeriya. Kamfanin man na Rasha na Gasprom ya tabbatar da haka lokacin da ya shaida haka ga kasashen biyu.

Tun farko gwamnatin Poland ta ce za ta kawo karshen amfani da gas daga Rasha na wani lokaci. Tuni kasashen biyu na nahiyar Turai da lamarin ya shafa suka bayyana cewa suna shirye da yanayin da suka samu kansu.

Ana ta bangaren ma'aikatar kula da tattalin arzikin kasar Jamus ta bukaci kwantar da jhankali kan abin da kasar take ciki wadda ta kasance daya daga cikin kasashen da ke ci gaba da dogaro da iskar gas daga Rasha. Wannan mataki na Rasha na da nasaba da irin tirjiyar da kasashen suna nuna bayan da kasar ta kaddamar da kutse a kan kasar Ukraine.

 


News Source:   DW (dw.com)