Rasha ta kakkabo jiragen yakin Ukraine 11

Ma'aikatar tsaron Rasha ta bayyana cewa ta kakkabo jirage marasa matuka mallakin Ukraine guda 11 da asubahin ranar Litinin bayan sun hari yankin Kursk da ke kan iyakar kasashen biyu da tsakiyar dare.

Har ila yau, makaman kare farmaki na Rashar sun lalata wasu karin jirage 5 a yankin Belgorod wanda shi ma ke iyaka da Ukraine, sai kuma wasu biyu a yankin Veronezh da ke da nisan daruruwan kilomita daga kudancin birnin Moscow kamar yadda ma'aikatar tsaron kasar ta wallafa a manhajar Telegram.

Rasha ta kai hari babban birnin Ukraine, Kyiv

Sai dai Rasha bata fadi adadin jirage marasa matuka da Ukraine din ta harba ba mata ba.

An shafe sama da shekara biyu ana yaki tsakanin Ukraine da Rasha inda aka samu asaran rayuka da kuma dukiya mai dumbin yawa.

 


News Source:   DW (dw.com)