Rasha ta ce 14 daga cikin jiragen marasa matuka ta kakkabo su ne a lardin Belgorod da ke kan iyakar kasar ta Rasha da Ukraine, yayin da biyu suka fada tekun Bahar Aswad, a cewar ma'aikatar tsaron Rasha a wani sako da ta wallafa a shafin Telegram.
Karin bayani: Rasha ta kai hari babban birnin Ukraine, Kyiv
Hare-haren na zuwa ne a daidai lokacin da Rasha ke cewa tana taba-alli da Kungiyar Tsaro ta NATO a wani taron gaggawa da zasu gudanar duk da cewa taron bai da nasaba da rage tasirin farmakin da ta ke yi ba a Ukraine, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Rasha RIA ta rawaito jawabin Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Rasha Alexander Grushko a fadar Kremlin.