Rasha ta kai sabbin hare hare yankunan Ukraine a daura da kudancin kogin Bahar Aswad yankunan da suka hada da Odesa da Mykolaiv.
Sojojin Ukraine sun ce Rasha ta kai hare haren ne da makamai masu linzami da ke cin dogon zango.
A yankin Odesa harin ya lalata gine-gine a wasu kauyuka na gabar kogi yayin da a Mykolaiv hare haren suka fada wani wuri na rumbin ajiya duk da yarjejeniyar da aka cimma ta bada damar wucewa da hatsi daga Ukraine ta kogin Bahar Aswad.