Rasha ta gamu da girgizar kasa mai karfin maki 5.9

Wata girgizar kasa mai karfin maki 5.9 ta auku a yankin Kamchatka na gabashin gabar tekun Rasha da safiyarJuma'a a cewar cibiyar da ke sanya ido kan aukuwar girgizar kasa ta Tarayyar Turai EMSC.

Cibiyar ta ce girgizar ta kai zurfin kilomita 51 sannan har yanzu bayanai basu gama bfitowa ba kan asarar da ta haddasa.

Girgizar kasa ta kashe mutane sama da 100 a kasar Nepal

Yankin  Kamchatka na Rasha mai yaki da Ukraine ya yi fice da tsaunuka da kuma duwatsu masu aman wuta da suke haddasa barna a wasu lokuta idan suka fara amayar da wutar cikinsu.

Girgizar kasa ta afku kusa da birnin New York

Akwai irin wadannan duwatsun sama da 300 a Kamchatka, kuma akwai yiwuwar  28 zuwa 36 daga cikinsu su amar da wutar a duk lokaci da suka tashi.

 


News Source:   DW (dw.com)