Rasha ta fara bincike kan dan jarida na Deutsche Welle

Rasha ta sanar cewa ta fara bincike kan wani mai aiko da rahotanni na kafar yada labarai ta Deutsche Welle da kuma  wata 'yar jaridar Ukraine wadanda aka kama suna aiki a yankin Kursk na Rasha da Ukraine ta mamaye. A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar tsaro ta FSB ta ce tana bincikar Nick Connolly na DW da kuma Natalia Nagornaya ta tashar 1+1 ta Ukraine.

Deutsche Welle: Shekaru 70 da kafuwa

Ana zargin 'yan jaridar da kutse cikin yankin Rasha ba tare da izini ba a lokacin da Ukraine ta rika kaddamar da hare-hare a yankin Kursk a farkon wannan watan na Agusta.

Baya ga daukar watanni Rasha na kutsawa a gabashin Ukraine da kuma shekara biyu da rabi na kaddamar da yaki kan Ukraine, Kyiv ta samu nasarar kutsawa cikin yankin Kursk na Rasha a ranar shida ga watan Agusta.

Shugaban Wikileaks Julian Assange ya shaki iskar yanci

Baya ga wadannan akwai kuma karin wasu 'yan jarida biyar da kasar ta ke bincike kansu wadanda kuma a yanzu haka ba su cikin Rasha. Idan aka same su da laifi za su iya shafe shekara biyar a gidan maza.


News Source:   DW (dw.com)