Magajin garin Moscow Sergei Sobyanin ya ce wannan na daya daga cikin manyan hare-hare da suka taba faruwa a birnin ta hanyar amfani da jirage marasa matuka. Sojojin na Ukraine sun tabbatar da kai hari kan na'urar kariya ta makami mai linzami samfurin S-300 da ke lardin Rostov a kudancin kasar Rasha.
Karin bayani:Shekaru 25 Putin na harkar mulki a Rasha
Jagoran sojojin Ukraine ya ce da irin wannan makami ne Rasha ta yi amfani wajen kai hari kan gine-ginen fararen hula a Ukraine. Sai dai mataimakin shugaban kwamitin sulhu na kasar Rasha Dmitry Medvedev ya nunar da cewa, kasarsa ba za ta tattauna da Ukraine ba, bayan da fadar mulki ta Kiev ta mamaye lardin Kursk na kasar Rasha.