Rasha ta dakatar da bai wa Latvia iskar gas

Rasha ta dakatar da bai wa Latvia iskar gas
Rasha ta bayyana kasa ta uku a nahiyar Turai da ta dakatar da cinikayyar iskar gas a tsakaninsu. Kamfanin Gazprom ya ce kasar ta saba ka'idar cinikayya da duk suka sanya wa hannu.

Kamfanin samar da iskar gas na kasar Rasha, ya sanar da dakatar da bai wa kasar Latvia makamashin saboda dalilai na karya ka'idojin kwantaragi da suka cimma.

Cikin wata takaitacciyar sanarwar da kamfanin Gazprom wanda mallakin gwamnati ta Rasha ne ya fitar, ya ce ba zai lamunce wa saba ka'idar da ya ce Latvia ta yi ba.

Da ma dai Rasha ta bukaci kasar ta Latvia da ke yankin Balkans ne da ta rika biyan kudin makamashin da kudaden Ruble, abin kuma da Latvia ta ki.

Kafin yanzu dai kamfanin na Gazprom ya dakatar da aika wa wasu kasashen Tarayyar Turai iskar ta gas da suka hada da Holland da Poland da Bulgaria saboda kememen biya da kudaden Ruble na Rasha da duk suka yi.


News Source:   DW (dw.com)