Rasha na dab da kwace iko da Mariupol

Rasha na dab da kwace iko da Mariupol
Sojojin Ukraine a birnin  Mariupol sun ƙi su mika wuya ga kiran da Rasha ta yi masu na su ba da kai bori ya hau.Sun kuma yi kira ga kasashen duniya da su agaza musu na ganin an tabbatar da tsaro.

Gwamnatin ta Ukraine ta yi kiran wata tattaunawa da Rasha domin cimma sulhu don ceton jama'ar da suka makale a birnin na Mariupol. Mai shiga tsakanin kana mai bai wa shugaban Ukraine shawara  ya ce ba tare da wani sharadi ba, suna shirye don gudanar da tattaunawa ta musamman domin samun damar kwashe fararan fula da sojojinsu. Kimanin fararen hula dubu dari ne suka makale a masana'antar sarrafa karafa ta Azovstal inda sojojin Ukraine suka ja daga a birnin da dakarun Rasha suka yi wa kawanya.


News Source:   DW (dw.com)