Rasha na ci gaba da matsa kaimi a Ukraine

Rasha na ci gaba da matsa kaimi a Ukraine
A daidai lokacin a aka shiga wata na hudu na yakin da ake yi a kasar Ukraine, sojojin kasar Rasha na kara zafafa hare-hare a kan wuraren da ke bijire musu a yankin Lugansk da ke gabashin kasar.

Sojojin Rasha na kokarin kewaye biranen Severodonetsk da Lyssytchansk, inda suke luguden wuta. Ma'aikatar tsaron Ukraine ta kuma ambaci kazamin fada da ake ci gaba da gwabzawa a kusa da yankunan Popasna da Bakhmout. Faduwar Bakhmut da ke lardin Donetsk zai bai wa Rashawa ikon wata mararrabar da ke zama cibiyar ba da izini ga yakin Ukraine.

Dakarun Ukraine sun bayana cewa suna fuskantar matsalolin wajen tinkarar sojojin Rasha a 'yan kwanakin nan a yankin Donbass da ya kunshi lardunan Lugansk da Donetsk. Dama dai shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi gargadin cewa "makonni masu zuwa na yaki za su kasance cikin wahala.".

   

   


News Source:   DW (dw.com)