Rasha: Girke makamai a Belarus

Rasha: Girke makamai a Belarus
Rasha za ta girke makaman da ke iya harba makamai masu linzami ciki har da na Nukiliya a Belarus nan da wasu watanni masu zuwa, a wani mataki na kara samun karfin fada aji da dafa wa Belarus.

Shugaba Vladimir Putine ne ya bayyana haka a wata ganawa ta keke da keke da takwaransa na Belarus Alexandre Loukachenko a birnin Saint-Pétersbourg a wannan Asabar, inda ya ce Rasha na shirin kara inganta jiragen Belarus ta yadda za su iya daukar makaman Nukiliya idan bukatar hakan ta taso, duk da takun sakar da kasar ke faman yi da manyan kasashen Yamma game da batun mamayar Ukraine.

Ganawar na zuwa ne a yayin da ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta ce sun karbe iko da Sievierodonetsk, bayan wani gumurzu da ya tilasta sojan Ukraine janyewa daga yankin mafi girma na gabashin Ukraine da kuma ke da matukar tasiri ga Rasha a ci gaba da mamayar da take yi a kasar. 


News Source:   DW (dw.com)