Da safiyar wanna rana ce aka bude bututun, sai dai babu tabbas game da adadin da za a ci gaba da yin jigila ta wannan bututu mai mahimmanci don guje wa rikicin makamashi a cikin hunturu.
Tun farko Rashar ta dakatar da isar gas din ne saboda gyaran injinn bututun. Jamus da ke dogaro da kusan kaso 60 zuwa 70 na cikin dari na makamashin iskar gas din kasar Rasha na zargin mahukuntan Kremlin da amfani da makamashin a matsayin makamin yaki.
Kamfanin iskar gas mallakar kasar Rasha na Gazprom ya rage kaso 40 cikin dari na makamashin da ya ke turowa Jamus a makwannin baya.
Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya sha alwashin kamfanin zai ci gaba da tsayawa a kan sharudan da suka cimma tun da farko na sayar da makamashin ga kasashen Turai, duk kuwa da takaddamar da ke tsakaninsu.