Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu ba zai fuskanci tuhuma ba kan badakalar kudaden da aka boye a wurin kiwonsa shekaru biyu da suka gabata, wanda ya kai 'yan sanda ga gudanar da bincike na musamman. Masu gabatar da kara na wannan kasa suka ce sun yi watsi da matakin gurfanar da Ramaphosa a gaban kuliya da ma dai duk wani da ke da hannu a lamarin saboda rashin isassun shaidu bayan cikakken bincike.
Karin bayani: Ramaphosa: Kafa gwamnatin hadaka abu ne mai kyau
Wannan badakalar da aka yi wa lakabi da "farmgate" ta shafi zargin cuwa-cuwar kudi dala 580,000 a gidan gonar shugaban kasar Afirka ta Kudu da wani mai tsaron lafiyarsa ya gano. An ce Cyril Ramaphosa ya boye makudan kudaden ne a cikin kujera domin kauce wa dokoki da kuma hukumomin binciken kudaden kasashen waje. A wancan lokaci, 'yan adawan Afirka sun yi amfani da wannan hujjar wajen neman a kada kuri’ar tsige shi, amma jam’iyyarsa ta ANC ta yi amfani da rinjayen da take da shi a majalisar dokokin kasar wajen dakile shirin ganin bayan Ramaphosa.