Raba gardama: An haramtawa zuri'ar Bongo tsayawa takara

Ministan Cikin Gida na kasar Hermann Immongault ya ce kaso 53.5% cikin dari na al'ummar kasar sun kada kuri'a a zaben raba gardama da aka gudanar, kuma kaso 91.8% cikin dari sun amince da sabon kundin tsarin mulkin. Kafofin yada labaran kasar sun ce ba a samu wani tashin hankali ba a yayin zaben duk da cewa an dan yi hatsaniya a wasu wurare.

Karin bayani: Gabon: Sojoji na shirya zaben raba gardama

Wasu daga cikin muhimman abubuwa da ke kunshe a daftarin da al'ummar kasar suka amince sun hadar da soke ofishin Firaminista da hana duk wani 'dan kasar dake da uwa 'yar kasar waje tsayawa takara wanda hakan zai haramta wa zuri'ar tsohon shugaban kasar da sojoji suka hambarar a bara Ali Bongo Ondimba tsayawa takara kasancewar matarsa 'yar kasar Faransa ce Sylvia Valentin Bongo Ondimba.

Karin bayani: Sabon sharadin takarar shugaban kasa a Gabon

Shugaban mulkin sojin kasar Janar Brice Oligui Nguema ya ce zaben raba gardamar kusan hanya ce ta dora kasar kan tafarkin dimukradiyya da ake sa ran gudanar da zabe a shekara ta 2025. An dai saki tsohon shugaban kasar a makon da ya gabata bisa dalilai na jinkai domin ya tafi kasashen ketare wajen duba lafiyarsa. Bongo ya hau kan mulkin kasar ta Gabon a shekara ta 2009, bayan mutuwar mahaifinsa Omar Bongo wanda ya shafe shekaru 41 a kan karagar mulkin kasar.

 


News Source:   DW (dw.com)