Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya kara yi wa kasashen yamma kashedi kan shirinsu na lafta wa Mosko karin takunkumi. Shugaban ya ce, zai mayar da martani mai zafi muddun kasashen yamma suka dauki matakin, ya kara da cewa, ko kadan kada a dauki kalamansa da wasa don a shirye ya ke, ya nakasa kasuwannin makamashin duniya.
Sabuwar takaddama ta kece, bayan da wakilin Mosko Sergei Lavarov a taron ministocin kasashen G20 da ke gudana a tsibirin Bali na kasar Indonesiya ya fice daga zauren taron saboda yadda ake caccakar kasar kan mamayar Ukraine, daga bisani, Rasha ta ce, somin tabi ne a hare-haren da take kai wa Ukraine, kalaman da suka kara fusata manyan kasashen na duniya.