Harinya lalata wani bangare na wata cibiyar soji, a cewar wani sabon rahoto na hukuma wanda ya ce addadin wadanda suka mutun na iya karuwa. Gwamnan yankin, Filip Pronine, ya ce har Hanzu wasu sauran mutane 18 suna a karkashi baraguzai na gine-gine da suka rikito.Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce makaman masu linzami guda biyu sun afkawa wani asibiti dake kusa da Poltava da kuma wata cibiyar illimi. Daya daga cikin gine-ginen Cibiyar Sadarwa da aka gina tun shekara ta 1960 domin horas da sojoji harkokin saddarwa ya lalace