Firanministan Poland, Donald Tusk ya ce kasar ita ce ke da cikakken hurumin sanin wanda zai shiga da kuma wanda zai fita daga Poland, kana zai gabatar da kudurinsa na dakatar da bayar da mafaka ga 'yan gudun hijira a gaban Majalisar dokokin kasar a mako na gaba.
Ko da yake bai yi karin bayani ba, Tusk ya ce hakan zai rage kwararar baki ba bisa ka'ida ba a Poland. Tun a shekarar 2021 ne Poland ke fama da shan matsin lamba kan 'yan gudun hijira a kan iyakarta da Belarus, inda gwamnatin kasar ke zargin kasashen Belarus da Rasha na amfani da 'yan gudun hijirar da suka fito daga yankin Gabas ta Tsakiya da kuma nahiyar Afirka wajen su tada zaune tsaye a kasashen yammacin Turai.