Pistorius ya yi zargin zagon kasa a lalata layukan sadarwa

Kazalika ministan tsaron Sweden Carl-Oskar Bohlin ya jaddada kalaman takwaransa na Jamus inda ya tabbatar da cewa akwai zagon kasa wajen lalata layukan sadarwar da tuni wasu daga cikin al'umma suka fara dandana radadin katsewar layukan.

Karin bayani: Rasha: Bude bututun Nord Stream 1

Katsewar layukan sadarwar ya faru ne shekara biyu da lalata bututun mai na karkashin kasa wato Nord Stream tun bayan kaddamar da yakin Rasha da Ukraine. A nashi martanin ministan tsaron Estonia, Hanno Pevkur ya ce takwaransa na Jamus Mr. Pistorious ya gaza kawo hujjar kai wa layukan sadarwar hari.

 


News Source:   DW (dw.com)