MInistan tsaron Jamus Boris Pistorius ya isa Kyiv domin tattauna karin taimakon tarayyar Turai ga kasar Ukraine sakamakon sauyin gwamnati a Amurka da ma watakila yiwuwar samun sauyin gwamnati a Jamus.
Pistorius ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Jamus dpa cewa abin da ke da muhimmanci a ziyarar shi ne jaddada kudirinsu na ci gaba da taimaka wa Ukraine.
Gabanin ya tashi zuwa Ukraine, a ranar Litinin, sai da ya gana da takwarorinsa na Poland da Amurka da Faransa da kuma Italiya a birnin Warsaw.
Kasashen biyar da suka hada da masu karfin soji a nahiyar Turai na kokarin tabbatar wa Ukraine da goyon tarayyar Turai ko da kuwa mai zai biyo bayan rantsar da Donald Trump.