Pelosi: Taiwan ta koka kan atisayen Chaina

Pelosi: Taiwan ta koka kan atisayen Chaina
Ziyarar kakakin majalisar wakilan Amirka Nancy Pelosi ta fusata hukumomin Chaina, inda suka kaddamar da wani atisayen sojoji na musamman a kusa da Taiwan bayan gargadin da suka yi tun da farko.

Shugabar kasar Taiwan Tsai Ing-wen ta gode wa kakakin majalisar wakilan Amirka Nancy Pelosi dangane da ziyar da take yi a kasar. Manyan jami'an guda biyu sun gana a safiyar Larabar nan, inda hukumomin Taiwan suka jinjina wa Pelosi a kan goyon bayan da ta nuna musu ta hanyar ziyartar tsuburin da Chaina ke ikirarin mallakinta ne.

 Ma'aikatar tsaron Taiwan ta siffanta atisayen da Beijing ta fara yi a kusa da kasarta matsayin cin fuska ga martabarta ta zama 'yan-tattar kasa. Amma av jawabin da Pelosin ta yi wa 'yan Taiwan ta ce ta isa kasar ne domin samar da zaman lafiya da kyautata abokantaka a tsakanin Amirka da Taiwan. 


News Source:   DW (dw.com)