Paparoma ya bukaci a tsagaita wuta a Ukraine

Paparoma ya bukaci a tsagaita wuta a Ukraine
A daidai lokacin da yaki tsakanin Ukraine da Rasha ke shiga wata na biyu, Paparoma Francis ya yi amfani da bikin Ista wajen yin kira ga masu fada aji na duniya da su ji koke-koken al'umma kan batun zaman lafiya.

A sakon da ya gabatar a wannan Lahadi albarkacin bukukuwan Ista, jagoran mabiya darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ya bayyana kaduwa kan yakin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine, inda ya nuna fatan ganin an tsagaita bude wuta don samun zaman lafiya. Paparoma ya ce: "Ba abin da muke gani sai zubar da jini da tashe-tashen hankula, zukatanmu cike suke da tsoro da fargaba a yayin da 'yan uwanmu maza da mata ke rufe kansu don tsira daga hare-haren bama-bamai."

Ko baya ga batun yakin Ukraine, rikice-rikice a sauran sassan duniya a kasashe irinsu Libiya da Yemen da Afghanistan da Habasha da Barma da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na daga cikin batutuwan da Paparoma ya mayar da hankali a kansu. A farkon watan Yulin wannan shekara ne ake sa ran jagoran dariyar Katolika na duniya zai kai wata ziyara a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.


News Source:   DW (dw.com)