A wata wasika da ya rubuta wa manyan limaman darikar ta Katolika da ke Amurka, Paparoma Francis ya ce shirin na Shugaba Trump abu ne da ke keta alfarmar dan Adam, inda a share guda ya shawarci limaman na Katokali da ke kasar da kada su bari a yi amfani da su wajen cin zarafi tare nuna wariya ga bakin haure.
Paparoman har wa yau ya ce rubuta wasikar da ya yi da ma jan hakalin limaman Katolikan na Amurka ya zama wajibi saboda a cewarsa mayar da bakin haure gida zai sanya wasu daga cikiinsu su shiga mummunan hali, saboda mafi akasarinsu sun bar kasashen nasu ne saboda talauci da rashi tsaro da yake-yake da matsalar gurbacewar muhalli da sauran abubuwa da ke barazana ga rayuwarsu.