Kotun kolin Pakistan ta yanke hukuncin cewa matakin da Firaminista Imran Khan ya dauka na rusa majalisar dokoki haramtacce ne ta kuma bada umarnin majalisar ta cigaba da shirinta na kada kuri'ar rashin amanna.
Kotun dai ta yi umarni majalisar ta dawo a ranar 9 ga wannan watan na Afrilu domin cigaba da kuri'ar rashin amannar.
Yan adawa sun ce suna da kuri'u 172 da ake bukata daga cikin kujerun majalisar dokokin 340 domin tsige Firaministan.