Pakistan: Zanga-zangar magoya bayan Imran Khan

Masu bore a Pakistan na neman a saki tsohon firanministan kasar, Imran Khan da sauran manbobin jam'iyyar PTI da aka kama, suna koma bukatar gwamnati mai ci ta yi murabus, saboda suna zargin an tafka magudi a lokacin zabe. Kazalika kasar ta dakatar da layukan waya da kuma internet a yankunan da ake da fargabar tsaro sakamakon zanga-zangar.

Karin bayani: Pakistan: Kotu ta bayar da belin Khan

A cikin faifayan bidiyon da ya wallafa, na hannun daman Mista Khan, Ali Amin Gandapur ya ce, Khan ya bukaci su tsaya a daidai wata mahada ta birnin da ake kira da D Chowk, har sun ga abun da ya ture wa buzu nadi wajen biya musu bukatunsu.

Mistan Khan da aka kada masa kuri'ar yanke kauna da gwamnatinsa a watan Afrilun shekarar 2022, na zaman gidan yari na tsawon shekaru uku tun a bara. Sai dai duk da tuhume-tuhumen laifuka 150 da ake masa ciki har da laifin cin hanci da rashawa da kuma tada zaune tsaye, har yanzu ludayinsa na kan dawo a siyasar Pakistan, inda magoya bayansa ke ganin zarge-zargen a matsayin wata kutungwila ta siyasa.

 


News Source:   DW (dw.com)