Majalisar dokokin Pakistan ta zabi Mohammad Shahbaz Sharif jagoran 'yan adawa a matsayin sbaon firamnista wanda ya maye gurbin Imran Khan da majalisar dokokin ta tsage a karshen mako.
Sabon Firaminista Mohammad Shahbaz Sharif yana da jan aiki farfado da tattalin arzikin kasar da samar da ci-gaban da ake bukata. Shi dai Shehbaz Sharif ya kasance dan uwa ga tsohon Firamini Nawaz Sharif wanda sau uku yana rike mukamun na firaminista.
Sharif ya lashe zaben zama firaministan kasar ta Pakistan da kuri'un 'yan majalisar dokoki 174 daga cikin 'yan majalisa 342.