Pakistan: Khan na iya zuwa gidan kaso

Pakistan: Khan na iya zuwa gidan kaso
Wata kotu a Pakistan za ta yi la'akari da daukar mataki kan tsohon firaministan kasar Imran Khan, biyo bayan jawabin da ya yi a karshen mako na barazana ga jami'an 'yan sanda da kuma wani mai shari'a.

Wannan na iya zama babbar barazana ga Mr Khan, mutumin da ke yakin neman sabon zabe, tun bayan da aka tilasta shi yin murabus a cikin wannan shekarar, kasancewar gurfanar da shi a gaban kotu na iya hana shi damar tsayawa takarar wani mukami.

Wani alkali mai ritaya, Shaiq Usmani, ya ce wannan babban laifi ne da zai iya janyo wa Imran Khan zaman kurkuku na tsawon watanni akalla shida, idan har an tabbatar da laifin akansa. Kana ba zai iya takarar neman wani mukami ba a Pakistan na tsawon shekaru biyar masu zuwa.

Wannan dai karin laifi ne kan zargin da ake masa a karkashin dokar yaki da ta'addanci, wanda tun da farko 'yan sanda suka gurfanar da shi a kai.


News Source:   DW (dw.com)