Tuni dai lardin ya rufe makarantun firamare a babban birnin kasar, Lahore, a wannan makon tare da haramta gudanar da wasu harkoki na taruwar jama'a. Mako guda kenan da mazauna lardin miliyan 14 ke zaune cikin wani hali na hazo da turnikewar hayaki mai gurbata muhalli. Punjab, da ke iyaka da Indiya, tana da mafi yawan manyan biranen kasar, inda kashi uku na mazaunan ba su kai shekaru 20.