Cholz ya ce ya ci tuwon fashi ne a kan tafiyar bayan da shugaba Volodymyr Zelensky ya ki amincewa da ziyarar shugaban kasar na Jamus Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier a Ukraine. Shugaban na Jamus da ke ziyara a birnin Warsaw na Poland ya so tare da shugabannin kasashen yankin Balkans su kai ziyara a Kiev amma shugaban kasar Ukraine ya ki amincewa. Saboda zargin da yayi masa na kawo cikas wajen shigar Ukraine cikin kungiyar tarrayar Turai a lokacin da yake rike da matsayin ministan harkokin wajen Jamus da kuma kusancinsa da Rasha.