Obama ya shaida wa dandazon jama'ar da suka halarci taron cewa Amurka ta shirya wa sabon babi da jin labari mai armashi da kuma shirya karbar shugaba Kamala Harris.
Obama ya kuma soki Donald Trump na Jam'iyyar Republican wanda ya gaje shi wanda kuma zai fafata da Kamala Harris a takarar neman kujerar shugabancin Amurka.
Tun da farko a ranar Talata 'yan Jam'iyyar Democrats sun tabbatar da Kamala a matsayin 'yar takarar shugabar kasa a karkashin inuwar Jam'iyyar a zaben da za a yi ranar 5 ga watan Nuwamba.
A ranar Alhamis Kamala Harris za ta gabatar da jawabi ranar da za a kammala taron na kwanki hudu.