Karamar minitar kudi ta Netherlands ta ajiye aiki a ranar Juma'a saboda zargin guda daga cikin abokan aikinta da yi mata kalaman nuna wariyar launin fata a lokacin taron majalisar ministoci kasar kan arangamar da aka yi tsakanin 'yan sanda da masu boren kin jinin Isra'ila a birnin Amsterdam.
Ko da shi ke murabus din nata bai yi barazanar wargaza gwamnatin hadaka da masu ra'ayin mazana jiya ke jagoranta ba, amma idan aka samu karin wasu ministoci suka bi sahuta hakan na iya haifar da rudani.
Ita dai Nora Achahbar 'yar asalin kasar Moroko mai shekaru 42 a duniya tsohuwar mai shigar da kara ce, kuma ta shiga cikin gwamnatin hadaka ta Netherlands a karkashin jam'iyyar NSC waddda ke da kujeru 20 a majalisa.
A lokacin da yake sanar da wannan labari firaministan Netherlands Dick Schoof ya yi watsi da hajjar ta Mme Achahbar ta gabatar domin ajiye aiki, inda ya ce ko kadan ba bu nuna wariyar launi fata a gwamnatisa.