Wannan shi ne karon farko da kamfanin na NNPCL ke daukar mai daga matatar ta Dangote, bayan daukar lokaci ana kokarin cimma matsaya a kan batun cinikin danyen mai.
Motocin dakon mai kusan 500 ne rahotanni suka tabbatar sun yi jerin gwano a harabar matatar, suna jiran daukar man fetur din ya zuwa kasuwa a Najeriya.
Daga ranar 1 ga watan Oktoba mahukunta a Najeriya sun ce kamfanin NNPCL zai fara bayar da gangar danyen mai 385 a duk rana domin tace shi daga matatar ta Dangote.
Ana fatan wannan matakin ya kawo karshen matsalar karancin mai da ma tsadarsa a Najeriya, kasar da ke da dimbin arzikin man fetur amma tun bayan janye tallafi mai da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi ya saka al'ummar kasar cikin wani mawuyacin hali.