Nijar ta yi tayin hako ma'adanin uranium ga kamfanonin Rasha

Jamhuriyar Nijar ta gayyaci kamfanonin Rasha zuwa kasar don gudanar da aikin hakar ma'adanin uranium da ma sauran albarkattun karkashin kasa, kamar yadda ministan ma'adanan kasar Ousmane Abarchi ya nema.

Karin bayani:Gwamnatin Nijar ta gargadi kamfanin ORANO

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya rawaito Mr Abarchi na cewa tuntuni suka gana da da kamfanonin da ke da sha'awar zuwa kasar don fara ayyukansu na hakar ma'adanan, ba wai uranium kadai ba, yana mai cewar babu damar barin kamfanonin Faransa su ci gaba da aiki a kasar, tunda ta nuna rashin amincewarta da gwamnatin mulkin sojinsu.

Karin bayani:Sojojin Rasha sun canji na Amurka a Nijar

Jamuhiyar Nijar ce ta 7 a duniya a arzikin uranium, kuma tun bayan juyin mulkin da sojojin suka yi a cikin watan Yulin bara suka raba gari da uwargijiyarsu Faransa, tare da fatattakar kamfanoninta da ke aiki a kasar.


News Source:   DW (dw.com)